7 Satumba 2020 - 11:57
Gwamnatin Kasar Faransa Ta Bada dalilan Wanzuwar Sojojinta A Kasar Mali

Ministan tsaron kasar Faransa Jean-Yves Le Drian, ya bayyana cewa wanzuwar sojojin kasar Faransa a kasar Mali don tabbatarb da tsaron kasar Faransa ne.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto ministan ya na fadar haka a jiya Lahadi a lokacinda yake magana dangane da kissan sojojin kasar guda biyu a kasar Mali a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata.

Kafin haka dai fadar Elize ta bada sanarwan mutuwar sojojin kasar Faransa biyu a kasar Mali a jiya Lahadi.

Har’ila yau ministan tsaron na kasar ta Farasna ya bukaci gwamnatin shugaba Emmanuel Macron ta matsawa sojojin da suka yi juyin mulki a kasar Mali lamba, don su gaggauta maida mulki ga fararen-hula a kasar.

Tun shekara ta 2013 ne gwamnatin kasar Faransa ta shigo da sojojinta kasar ta Mali da sunan yaki da ‘yan ta’adda wadanda suke mamaye da arewacin kasar a lokacin.

342/